in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun bukaci taimakon kasa da kasa game da batun tabbatar da zaman lafiya da tsaro
2017-09-23 12:51:05 cri
A ranar Juma'a kasashen Afrika suka nemi taimakon kasa da kasa domin tabbatar da zaman lafiya da ayyukan jin kan bil adama a kasashensu, sun yi wannan kira ne a lokacin babban taron MDD da aka saba yi a duk shekara.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya bayyana cewa batun zaman lafiya ya kasance wani batu dake fuskantar babbar barazana a kasashen Afrika, musamma idan aka yi la'akari da matsalolin da suka hada da yawaitar ayyukan ta'addanci, tashe tashen hankula, talauci da matsalar sauyin yanayi.

Paul Biya ya yi Allah wadai da karuwar tashe tashen hankula da ake samu a nahiyar Afrika, da Asiya, da Latin Amurka da kuma yankin gabas ta tsakiya, wadanda ke haifar da tabarbarewar al'amurra da jefa al'umma cikin matsanancin hali. Ya ce jamhuriayr Kamaru ta karba kuma tana cigaba da karbar bakuncin dubun dubatar 'yan gudun hijira daga jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma Najeriya.

Biya, ya bukaci dukkanin kasashen duniya su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiyar duniya, kana ya bukaci kasashen duniyar dasu dauki wannan sako na Afrika da muhimmancin gaske.

Da yake karin haske game da kalaman na mista Biya, shugaban jamhuriyar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadera, ya nanata muhimmancin aza tubulin tabbatar da zaman lafiya da kuma warware duk wata takaddama ta hanyar tattaunawar sulhu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China