Cikin umarnin da ya rubuta ga taron rage fatara ta hanyar sauya matsugunan jama'a da aka kammala a jiya, Firaministan ya ce dole ne aikin ya kasance bisa tsari da adalci.
Da yake bayyana rage talauci ta hanyar sauya matsugunan jama'a a matsayin jigo wajen rage fatara da sake fasali a kasar, Li Keqiang ya ce ya kamata hukumomi su tabbatar da ingancin aikin tare da inganta kula da harkokin kudi.
Ya kuma bukaci hukumomi su taimakawa wadanda aka sauyawa muhallan, ta hanyar bunkasa masana'antu da kara musu hanyoyin samun kudin shiga, saboda a tabbatar da kowane iyali ya fita da kangin talauci bayan sauya muhallin.
A bana, kasar Sin ta shirya rage yawan al'ummarta dake fama da talauci da sama da miliyan 10, ciki har da miliyan 3.4 da za a sauyawa masugunai. (Fa'iza Mustapha)