in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin yaki da kwararowar hamada
2017-09-21 07:56:11 cri

A kwanakin baya ne, aka gudanar da taron kasashe sama da dari da suka sanya hannu a kan yarjejeniyar hana kwararowar Hamada karo na 13 a birnin Erdox dake jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Masana da kungiyoyin kasa da kasa sun yaba matakai da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin yaki da kwararowar Hamada. Kasar Sin dai ta yi amfani da batun Hamada wajen samar da ayyukan yi ta hanyar dashen itatuwa a yankunan Hamada na kasar, wani mataki na yaki da talauci.

Yayin da wasu sassan duniya ke fama da matsalar kwararowar Hamada, wani rahoton hukumar kare muhalli ta MDD ya nuna cewa, kasar Sin ta dasa bishiyoyi a wasu yankunan hamadar Kubuqi, wadanda fadinsu ya kai eka miliyan 9.69.

Haka kuma kasar Sin ta samar da kayayyaki a wannan aiki da darajarsu ta kai RMB biliyan 500, gami da fitar da jama'a fiye da dubu 500 daga kangin talauci.

Taron ya sake jaddada bukatar hada kai ta hanyar musayar bayanai da fasahohi wajen yaki da Hamada da raya tattalin arziki, maimakin barin matsalar ta kawo illa ga rayuwar al'umma.(Saminu,Fa'iza,Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China