in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya tattauna ta wayar tarho da Macron game da yanayin Zirin Koriya
2017-09-08 19:05:58 cri

A Yau Jumma'a ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron game da yanayin da ake ciki a Zirin Koriya, inda ya jaddada matsayin kasar Sin game da kawar da makaman nulkiya a zirin na Koriya.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, hanya guda ta kawo karshen wannan matsala cikin lumana ita ce tattaunawa mai ma'ana da kuma sasantawa, Yana mai fatan cewa, kasar Faransa kasancewarta mai kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, za ta taka muhimmiyar rawa wajen sassauta lamarin tare da ganin an farfado da tattaunawa.

A nasa bangaren shugaba Macro ya ce kasarsa ta himmatu wajen ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya. Kana tana dora muhimmanci game da matsayi da gagarumar rawar da kasar Sin take takawa na ganin an warware batun nukiliyar Zirin koriya ta hanyar da ta dace. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China