in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan Badminton
2017-09-06 20:37:19 cri
Tarihin wasan badminton
Game da tarihin wasan badminton, an ce a da, mutanen da suka zauna a nahiyoyin Turai da Asiya, sun dade suna wasa da shuttlecock, wato kwallon wasan badminton wanda ake yi da gashin tsuntsu. Amma ba a fara yin wasan badminton na zamani a lokacin ba, sai zuwa tsakiyar karnin 19.
An ce a shekarar 1860, an buga wani littafin a birnin London na kasar Birtaniya, wanda ya yi bayani kan wasan badminton. Kafin hakan, watakila su hafsoshi 'yan Birtaniya da suka zauna a yankin Indiya da kasarsu take mulkin mallaka a lokacin, su ne suka fara wasan badminton. Dalilin haka shi ne, wasan ya fara farin jini a Indiya a shekarun 1870. Musamman ma a wani garin da ake kira Poona, wanda ya kasance a yammacin Indiya, inda wasan badminton ya samu karbuwa sosai, har ma aka rubuta cikakken tsarin wasan a can a shekara ta 1873. Zuwa shekarar 1875, wasu hafsoshin da suka yi ritaya daga Indiya sun koma Birtaniya, inda suka kuma kafa kulob din wasan badminton na farko a garin Folkestone na kasar.
Da farko dai, ana wasan ne tsakanin mutane daya-daya, ko kuma mutane biyu biyu, ko uku uku ko hudu-hudu. Kafin daga bisani a gano cewa wasannin da suka gudana tsakanin 'yan wasa daya-daya, ko kuma biyu-biyu kadai sun fi dacewa. Zuwa shekarar 1893, kungiyar wasan badminton ta Ingila ta kaddamar da sabon tsarin wasan badminton, wanda aka samu bisa daidaita tsohon tsari irin na Poona, ta kuma karbi bakuncin gasar badminton ta farko a shekarar 1899.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China