Mataimakin Manajan rukunin filin jirgin saman Hubei Gan Xiangtian, ya ce ana sa ran zauren na 3, na filin jirgin saman kasa da kasa na Wuhan na Tianhe, wanda ya lakume yuan biliyan 40 kwatankwacin dala biliyan 6, zai dauki matafiya miliyan 35 a ko wacce shekara zuwa shekarar 2020.
Sannan kayakin da za a wuce da su ta cikin zauren za su kai ton 440,000 a ko wacce shekara.
Yayin da za a yi wa zaure na 1 da na 2 na filin jirgin saman kwaskwarima don tashin jirage na musamma da masu arahar farashi, za a yi amfani da sabon zauren wajen tafiye-tafiyen da suka shafi na cikin gida da kasashen waje.
Baya ga zauren, an kuma bude sabuwar cibiyar sufuri a filin, wanda ke samar da hanyar jirgin karkashin kasa da ta motocin safa da na tasi.
Filin jirgin saman na Tianhe ya samu fasinjoji miliyan 20.8 a bara, adadin da ya karu da kaso 9.6 a kan na 2015.
Bugu da kari, jirage na tashi daga filin zuwa birane 47 dake kasashe 24. (Fa'iza Mustapha)