in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta doke Senegal a wasan karshe na gasar kwallon Kwando ajin mata ta Afirka
2017-08-31 10:52:39 cri
Kungiyar 'yan wasan kwallon Kwando mata na Najeriya, sun lashe kofin gasar nahiyar Afirka na shekarar 2017. Karo na 3 ke nan Najeriyar na daukar wannan kofi.

A wasan karshe da suka buga ranar Lahadi, Najeriya ta doke Senegal da maki 65 da 48, yayin wasan da aka fafata a birnin Bamako na kasar Mali. Bayan kammala gasar, 'yar wasan Senegal Astou Traore ta samu lambar yabo ya wadda ta fi zura kwallaye a raga da mai 17 duk da kasar ta bata samu damar daukar kofin ba. Mali ita ce ta zo na 3 a gasar ta bana da lambar tagulla, bayan da ta doke Mozambique da maki 75 da 52, a wasan su na neman matsayi na 3.

Hukumar FIBA ke shirya wannan gasa, wadda kuma ke da mambobi daga kasashe da yankuna 213.

Yanzu haka dai Najeriya da Senegal din ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar kwallon Kwando ta duniya da za a gudanar a kasar Sifaniya a shekarar 2018 mai zuwa.

Kafin dai wasannin zagayen karshe, Angola ta doke Cameroon da ci 78 da 56, ta kuma lashe wasan ta da Mali da maki 68 da 59. Kaza lika ta lallasa Tunisia da maki 62 da 55, kana ta doke Cote d'Ivoire da maki 70 da 62 inda ta zamo ta daya a rukunin A.

A rukunin B kuwa, Najeriya ta doke Senegal da ci 58 da 54, a wasan su na ranar Laraba. Ita ma tawagar ta Najeriya ita ce ke kan gaba a rukunin na B, inda ta lashe dukkanin wasannin ta na rukunin. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China