in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da cibiyar nazarin harkokin Najeriya a jami'ar horas da dalibai ta Zhejiang
2017-08-24 15:33:30 cri

A ranar 12 ga watan Agustan sherarar 2017 ne, tsohon ministan tsaron Najeriya Laftana janar Aliyu Mohammed Gusau mai ritaya ya kaddamar da cibiyar nazarin harkokin Najeriya gami da taron karawa juna sani kan hadin gwiwar Sin da tarayyar Najeriya a jami'ar horar da malamai dake birnin Jinhua na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, wato Zhejiang Normal University.

Cibiyar wadda ita ce irinta ta farko tsakanin jami'o'in kasar Sin za ta mayar da hankali ne wajen nazartar fannoni Ilimi, al'adu, kabilun Najeriya, addinai da hadin gwiwar Sin da Najeriya. A daya hannun kuma, taron karawa juna sanin da aka gudanar yayin kaddamar da wannan cibiya ya samu halartar wakilan kamfanonin kasar Sin dake Najeriya da wakilin rundunar sojojin kasar Sin da dalibai daga bangarorin biyu dake nazarin harkokin Afirka da Najeriya.

Taron ya kuma tattauna a kan batutuwan tsaro, zuba jari da cinikayya tsakanin sassan biyu, da kuma matakan kare kadarorin da sassan biyu suka zuba jari a kasashen juna.

Masana na kallon kafa cibiyar a matsayin wani muhimmin mataki da zai karfafa hadin gwiwar Sin da Najeriya daga dukkan fannoni. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China