A baya, Ma'aikatar lafiya ta kasar, ta sanar da cewa, mutane 36 ne suka mutu kuma sama da 120 sun jikkata sanadiyyar taho-mu-gama da wasu jiragen kasa biyu suka yi a gabashin birnin Alexandria.
Sai dai, Ma'aikatar ta ce adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su ka iya karuwa la'akari da munanan raunuka da mutane suka samu.
Da safiyar jiya Juma'a ne, wani jirgin kasa da ya fito daga Cairo zuwa Alexandria, ya kutsa kai bayan wani jirgi da shima ke kan hanyarsa ta zuwa Alexandria, abun da ya yi sanadin mutuwa da jikkatar gomman mutane. (Fa'iza Mustapha)