Hukumar 'yan sandan Najeriya ta karyata ikirarin da mayakan 'yan tada kayar baya na Boko Haram ta yi na cewar ta yi garkuwa da jami'an 'yan sanda mata 10 a makon jiya a jihar Borno dake arewa masu gabashin kasar.
A wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Alhamis ya nuna cewa, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Borno Victor Isuku, ya yi watsi da ikirarin da mayakan suka yi.
A wani faifan bidiyo da wasu jaridun kasar suka bibiya a shafukan internet a ranar Talata, an gano wani mutum dake bayyana kansa a matsayin shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, ya bayyana cewa akwai jami'an tsaro mata su 10 dake hannun mayakan 'yan tada kayar bayan.(Ahmad Fagam)