Ma'aikatar ilmin bai daya ta Sudan ta kudu ta kaddamar da wani shiri da kungiyar EU ta dauki nauyinsa wanda ya tasamma dalar Amurka miliyan 22.7, inda za'a dinga biyan dala 40 ga kowane malamin makarantar firamare a kasar wanda yawansu ya kai dubu 30 a matsayin kudaden alawus.
Ministan ilmin kasar Deng Deng Hoc, ya shedawa 'yan jaridu cewa, ma'aikatar tare da hadin gwiwar hukumomin hulda na kasa da kasa za su fara biyan kudaden ga malaman makarantun kimanin 16,000 a cikin wannan mako, da nufin baiwa malaman kwarin gwiwa don su samu damar ci gaba da karantar da daliban kasar a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin komadar tattalin arziki da tabarbarewar tsaro.(Ahmad Fagam)