in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi jawabi a babban taron shawarwari kan rage talauci tsakanin Sin da kasashen Afirka
2017-06-22 13:24:23 cri

A jiya Talata ne, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya gabatar da jawabi a taron shawarwari kan rage talauci tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana da bikin bude dandalin tattaunawar masu ba da shawara tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya bayyana cewa a taron shawarwari kan rage talauci tsakanin Sin da kasashen Afirka, da bikin bude dandalin tattaunawar masu ba da shawara tsakanin kasashen biyu, cewar ya yi farin ciki da ziyarar da ya kawo cibiyar taron kungiyar AU, domin halartar wannan taro. A madadin gwamnatin kasar Sin, Wang Yi ya yi maraba da zuwan mahalarta taron duka, kana ya taya murnar kaddamar da taron da fatan za a samu cikakken nasara.

Wannan ne karo na 12 da Wang Yi ya kai ziyara a nahiyar Afirka tun bayan da ya hau kujerar ministan harkokin wajen Sin, baki daya ya ziyarci kasashen Afirka 31, inda ya fahimci hakikanin yanayin da ake ciki a wannan nahiya, da tabbatar da bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Sin tana ganin cewa, karnin 21 da ake ciki, ba ma kawai na nahiyar Asiya ba ne, har da nahiyar Afirka, da kuma kasashe masu tasowa.

Yanzu haka duniya na fama da matsalolin zaman lafiya da bunkasuwa. Al'ummar Afirka sama da miliyan 400 suna fama da talauci, yayin da al'ummar Sin sama da miliyan 40 ke kokarin fita daga kangin talauci. A sabili da haka, yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannin kawar da talauci ya zama babban nauyin dake bisa wuyanmu.

Wang ya ce, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, kamata ya yi mu yi kokarin biyan bukatun kasashen Afirka, mu hade bunkasuwar Sin da ta nahiyar Afirka a waje daya, domin neman samun ci gaba da annashuwa tare. Wang ya halarci taron ne tare da shugaban hukumar zartarwar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, da zummar yin musayar ra'ayoyi da fasahohi da masu ba da shawara da masana da kafofin yada labarai na Sin da kasashen Afirka, kan yadda za a rage talauci a Afirka, da sa kaimi ga hadin gwiwa da samun moriyar juna tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Bayan haka, Wang ya kara da cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi, kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yi alkawarin cewa, ya zuwa shekarar 2020, wato shekarar cika shekaru 100 da kafa jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, za a kammala aikin kafa zamantakewar al'umma mai jituwa a Sin, kana wani muhimman bangare daga ciki shi ne aikin rage talauci a dukkan fannoni. Game da wannan batu, dole ne a tsaya kan manufofi hudu, wato ta farko, tsayawa tsayin daka da kuma yin amfani da fifikon da ake da shi. Na biyu, tsayawa tsayin daka kan neman samun ci gaba. Na uku, neman samun bunkasuwa ta hanyoyi daban daban bisa bambanci da ake da shi. Na hudu, tsayawa tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida.

Yanzu an shiga sabon yanayi na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. A watan Disamba na shekarar 2015, an yi nasarar gudanar da taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda ya bude sabon babi na yin hadin gwiwar samun moriyar juna da samun ci gaba tare tsakanin sassan biyu. A yayin taron kolin, shugaba Xi Jinping ya gabatar da Shirin hadin gwiwa a fannoni goma da ake fatan aiwatarwa cikin shekaru uku masu zuwa, ciki har da shirin hadin gwiwa game da rage talauci, wanda ya mai da hankali ga bukatun kasashen Afirka yadda ya kamata. A watan Mayun bana, an gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar"Ziri daya da hanya daya" a birnin Beijing tare da samun babbar nasara, taron da ya karfafa matakan yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Sin na fatan za a yi amfani da shawarar raya "Ziri daya da hanya daya", domin hade "Shirin hadin gwiwa a fannoni goma tsakanin Sin da kasashen Afirka" da "shirin raya kasashe Afirka nan da shekarar 2063" da kungiyar AU ta gabatar. Ana fatan kasashen Afirka za su sami ci gaba da kansu ta hanyar zurfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za ta fidda da kanta daga talauci cikin sauri.

Game da wannan batu, Wang Yi ya furta cewa, da farko, Sin na fatan yin musayar ra'ayoyi da fasahohi da kasashen Afirka kan shirye-shiryen rage talauci da suke bukata. Na biyu, Sin na fatan samun ci gaba tare da kasashen Afirka, domin taimakawa wajen daidaita matsalolin karancin muhimman kayayyakin jin dadin rayuwar jama'a da kwararru da kuma kudade. Na uku, Sin za ta samar da yanayi mai kyau na rage talauci ga kasashen Afirka, ta hanyar taimaka musu wajen kara karfinsu a fannonin tsaro da tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta'addanci da sauransu. Na hudu, sa kaimi ga kasashen duniya wajen taimakawa kasashen Afirka ta yadda za su hanzarta rage talauci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China