Mr. Ross ya fadi hakan ne a yayin da yake jawabi a wani bikin liyafar da babbar kungiyar 'yan kasuwa ta Sinawa dake kasar Amurka ta shirya wa masu zuba jari a kasar. Kazalika, Mr. Ross ya gode wa tawagar wakilan mazu zuba jari na kasar Sin wadanda suka halarci taron koli na zuba jari mai jigon "Zabin Amurka" na shekarar 2017.
A tsakanin ranekun 18 da 20 ga watan nan na Yuni ne ake taron koli na zuba jari mai jigon "Zabin Amurka" na shekarar 2017, a jihar Mariland dake kusa da birnin Washington DC, fadar mulkin kasar Amurka.
Bisa umarnin matakin farfado da sana'o'in kere-keren kasar Amurka da shugaba Donald Trump ya gabatar, yanzu haka daga gwamnatin tarayyar zuwa kananan hukumomi na gwamnatoci a matakai daban daban dake kasar Amurka, na kokarin jawo jarin waje da kuma 'yan kasuwa baki, tare da kokarin kafa wani kyakkyawan yanayi na shigar da jarin waje cikin kasar. (Sanusi Chen)