Ma'aikatar kudi ta kasar da ta bayyana haka a jiya Litinin, ta ce wannan ya kawo kudin da aka ware na rage fatara a matakin kananan hukumomi a bana zuwa kusan yuan biliyan 86.1.
Gwamnatin kasar Sin dai ta lashi takobin kawar da fatara tsakanin jama'arta nan zuwa shekarar 2020, domin samar da al'umma mai matsakaicin ci gaba.
A shekarar 2016 kadai, kasar Sin ta taimaka wajen fitar da mazauna kauyuka miliyan 12.4 daga kangin talauci.
Zuwa karshen shekarar 2016, mutane miliyan 43.35 ne ke cikin fatara a kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)