Hua Chunying ta ce tuni ofishin jakadancin kasar Sin dake Pakistan, ya fara gudanar da binciken gaggawa da hadin gwiwar mahukuntan kasar ta Pakistan, a wani mataki na tabbatar da kubutar da Sinawan da aka yi garkuwa da su.
Sai dai a hannu guda uwar gida Hua, ta ce bangaren Pakistan ya riga ya shaidawa Sin cewa, mai yiwuwa ne masu garkuwa da mutanen sun riga sun hallaka su.
Ta ce kasar Sin na matukar adawa da duk wani nau'in aiki na ta'addanci, za kuma ta ci gaba da hada kai da Pakistan, a duk wani mataki na yaki da ayyukan 'yan ta'adda da kuma tabbatar da tsaro da daidaito a kasar.