Mai rikon mukamin ministan lafiyar yankin Riziki Pemba Juma ce ta bayyana hakan, tana mai cewa ma'aikatar lafiya ta lura da yadda rashin tsafta, wadda ambaliyar ruwa da ta afkawa yankin ya haifar, na haddasa yaduwar wannan cuta mai matukar hadari.
Bisa al'ada dai al'ummar yankin na Zanzibar wadanda mafi yawan su musulmi ne, na gayyatar juna cin abincin bude-baki a wannan wata na Azumin Ramadan, sai dai a wannan karo gwamnatin yankin ta bukaci al'umma da su dakatar da hakan, domin kaucewa abun da ka je ya zo.
A cewar jami'ar, an riga an gano mutane 23 da cutar ta amai da gudawa ta kama a yankin, wanda hakan ya sanya mahukunta ta kebe wani sansani na musamman, domin baiwa wadanda suka kamu da ita kulawar da ta dace. (Saminu Hassan)