Jami'in kula da harkokin al'adu na kasar Sin dake Nijeriya Li Xuda, ya ce cibiyar al'adu ta kasar Sin dake Nijeriya ce ta shirya baje kolin da za a shafe kwanaki 7 ana yi, mai taken " kasar Sin a idanun 'Yan Nijeriya' da nufin ba da dama ga wadanda ba su taba zuwa ba, kara fahimtar kasar dake nahiyar Asiya.
Masu fasaha da dama ne su ka baje ayyukansu dake bayani game da rayuwarsu a kasar Sin da kuma yadda suka dauki kasar da tafi kowanne yawan al'umma a duniya.
Daga cikin ayyukan akwai zane-zane, da ginin gumaka da hotuna da kayan karau da dai sauransu.
Bikin bude baje kolin ya samu halartar wakilai daga kasar Sin, da jami'an ofishin jakadancin kasar, da jami'an Nijeriya, da masu fasaha da 'yan jarida da kuma 'yan Nijeriya da dama da ofishin jakadancin ya dauki nauyin kawo su kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)