in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faidar shawarar ziri daya da hanya daya ga ci gaban duniya
2017-05-18 12:35:41 cri

Da yammacin ranar Litinin 15 ga wata ne aka rufe taron kolin dandalin tattaunawa kan shawarar "ziri daya da hanya daya", wanda aka yi kwanaki 2 ana yinsa a nan Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A lokacin wannan taro mahalartansa sun cimma matsaya daya, a bangarori daban daban, an kuma samu hanyar yin hadin gwiwar kasa da kasa, da yadda za a aiwatar da shirin bunkasa "ziri daya da hanya daya". Bugu da kari, a yayin taron, bangarori daban daban daga kasashen duniya sun nuna kyakkyawar alamar kokarin yin hadin gwiwar ciyar da bil Adama gaba, ta hanyar bunkasa "ziri daya da hanya daya".

A yayin taron na kwanaki biyu, muhimman baki daga cikin gida da waje fiye da 1500 ne suka tattauna bisa jigon taron, wato "kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin bunkasa 'ziri daya hanya daya' tare, ta yadda za a samu ci gaba tare".

Bayan da shugaba Xi Jinping ya fitar da wannan shawara ta "ziri daya da hanya daya" a shekarar 2013, bisa ka'idar tattaunawa, da bunkasa, da kuma rarrabawa tare", bangarori daban daban wadanda suka amsa wannan shawara sun yi kokarin yin hadin gwiwa a fannonin daidaita manufofi, da hanzarta aiwatar da ayyukan tattalin arziki da cinikayya, da hade kayayyakin more rayuwar jama'a, da kuma saukaka sharuddan cinikayya da zuba jari. Al'ummomin kasa da kasa ma na kara yin mu'amala a tsakaninsu. Ya zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa kimanin 68 ne suka amince da takardun hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin.

A karshe, kasar Sin ta sanar da sake shirya karo na biyu na taron kolin shawarar "ziri daya da hanya daya" a shekarar 2019. (Ahmed, Saminu, Ibarhim /Sanisu Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China