Ma'aunin karfin tattalin arzikin (GDP) na kungiyar hadin kan tattalin arziki na kasashen Asiya da Pacific wato (APEC) a takaice, zai samu karuwar kashi 3.8 bisa 100 tsakanin shekarar 2017 zuwa ta 2018, wanda ya dara karuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Hasashen na baya bayan nan wanda sashen kididdiga na kungiyar APEC ya fitar, mai taken "Dunkulewar duniya: Kyau da rashin kyau da kuma tsarin gudanarwa" wanda sashen tsare tsare na kungiyar APEC, PSU ya ya fita a yau Laraba.(Ahmad Fagam)