in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Agazawa mata ta yadda za su samu abin dogaro da kansu
2017-05-24 07:06:39 cri

A shirin na yau, za a tattauna kan yadda za a agazawa mata ta yadda za su samu abin dogaro da kansu.

Gaskiya dai, mata sune iyaye, kuma suke kula da gida. Amma sakamakon ci gaban zamani, yanzu matsayin mata ya canja sosai, wato yanzu sun bar dogara da maza sun koma neman samun 'yancin kansu, daga lura da yara, kula da ayyukan gida kawai zuwa sa hannu cikin ayyukan raya kasa da kuma gudanar da harkokin duk kasa.

Ganin muhimmiyar rawa da mata ke takawa wajen ci gaban duniya, hukumar kula da harkokin da suka shafi hakkin mata da daidaiton jinsi ta Majalisar Dinkin Duniya wato UN Women kan tsara wani babban take a ko wace shekara domin kara kaimi ga ci gaban sha'anin mata a fannoni daban daban. Taken Ranar mata a bana na mayar da hankali ne "kan rawar da mata ke takawa a fagen ayyukansu la'akari sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, a kokarin tabbatar da daidaiton jinsi nan zuwa shekarar 2030".(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China