in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar UNESCO: shirin " ziri daya da hanya daya" na da ma'ana
2017-04-19 13:50:46 cri

Za a gudanar da dandalin tattaunawa na manyan jami'ai na kasashe daban daban game da shirin "ziri daya da hanya daya" a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a watan Mayu mai zuwa. Kafin haka, babbar darektar hukumar raya ilimi da al'adu ta UNESCO, Madam Irina Bokova, wadda ita ma za ta halarci dandalin da zai gudana a Beijing, ta bayyana ra'ayinta dangane da shirin "ziri daya da hanya daya".

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin hadin gwiwar kasa da kasa na "ziri daya da hanya daya" a shekarar 2013, da zummar kara hadin kai tsakanin kasashen Asiya, Turai, da kasashen Afirka, musamman ma a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwa, da tattalin arziki, da kuma al'adu. Dangane da shirin, madam Bokova ta ce, kasashe fiye da 40 sun riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin, lamarin da ya nuna yadda shirin yake samun karbuwa sosai a duniya. Sa'an nan ita kanta da hukumar UNESCO dukkansu suna goyon bayan shirin sosai. Ta ce,

"A zamanin da muke ciki, ana bukatar samun karin shirye-shirye irin wannan shirin na 'ziri daya da hanya daya', wadanda za su taimaka mana wajen tantance harkar zuba jari da huldar tattalin arziki. Haka zalika ya kamata mu lura da karin musayar ra'ayi da ake samu tsakanin al'adu daban daban. Saboda haka hukumar UNESCO tana goyon bayan shirin 'ziri daya da hanya daya' matuka."

A shekarar 2015, madam Irina Bokova ta taba kai ziyara a lardin Shaan'xi na kasar Sin, wanda ya kasance wurin mafarin 'hanyar siliki'. Da hukumar ta UNESCO ta sanya 'hanyar siliki', wadda ake bi wajen jigilar kayayyaki tsakanin kasar Sin da sauran kasashen dake yamma tun shekaru 2000 da suka wuce, cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi masu daraja a duniya. A ganin madam Bokova, "hanyar siliki" ta taka muhimmiyar rawa wajen mu'ammalar da aka yi tsakanin al'ummomi daban daban a tarihin dan Adam. A cewarta,

"Hanyar siliki ta fara daga birnin Xi'an dake yammacin kasar Sin, ta bi ta yankunan gabas ta tsakiya, da Turai, har zuwa nahiyar Afirka. Ta haka za mu iya ganin cewa, ya fara daga shekaru 2000 da suka wuce, an riga an samu nasara wajen mu'amala tsakanin al'ummomi daban daban na duniya. Har zuwa yanzu, 'hanyar siliki' ta ba mu darrusa masu yawa, musamman ma a fannonin neman ci gaba, da karin musayar ra'ayi tsakanin kasashe daban daban, gami da samun fahimtar juna tsakanin mutane."

Madam Bokova ta ce a zamanin da muke ciki na fuskantar barazanar ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, shirin "ziri daya da hanya daya" na da ma'ana matuka. A cewar ta,

"Shirin nan ya shafi bayanai da yawa a fannonin musayar ra'ayi, da yunkurin kiyaye al'adu daban daban na duniya, kuma ya shafi kokarinmu na neman cigaba da walwala. Yana da ma'ana sosai a wannan zamani da muke ciki. Domin har yanzu ana fama da masu tsattsauran ra'ayi, wadanda suka lalata wurin ibada na addinin Buddah dake Afghanistan, kawai domin ba su son ganin kasancewar al'adu daban daban a duniya. Kuma ana samun karin wadannan munanan ayyuka a kasashen Iraki da Syria."

Hukumar UNESCO a nata bangare ta dade tana kokarin kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu a duniya. Yayin da ta ambaci ayyuka a wannan fanni, madam Bokova ta yabawa kasar Sin kan gudunmowar da ta samar wajen tallafawa aikin hukumarta. Ta ce,

"Ina so na sake godewa gwamnatin kasar Sin, kan yadda ta jefa kuri'ar amincewa kan wani kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas da shi a watan Maris da ya wuce, wanda ya shafi niyyar tabbatar da zaman lafiya a duniya, da kokarin kiyaye kayayyakin tarihi da al'adu daban daban. Kudurin ya nuna yadda aka fara kula da ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi, da musayar ra'ayi tsakanin al'adu daban daban, cikin harkokin siyasa da ake kula da su a duniya. Wannan ya dace da burin da kasar Sin take neman cikawa bisa gabatar da shirin 'ziri daya da hanya daya'."

A karshe, madam Bokova ta ce, tana sa ran ganin shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi wani jawabi mai muhimmanci a wajen dandalin da za a kira a birnin Beijing.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China