in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: yadda habakar samar da hajoji da bada hidima ke jan kafa ka iya barazana ga hada-hadar kudi da daidaiton zamantakewar al'umma
2017-04-05 13:37:57 cri
Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya yi gargadin cewa, yadda habakar samar da hajoji da bada hidima ke jan kafa tun daga matsalar kudi da aka shiga a shekarar 2008, ka iya barazana ga hada-hadar kudi da daidaiton zamantakewar al'umma a wasu kasashe.

Babbar Daraktar Assusun Christine Lagarde wadda ta bayyana haka yayin wani taro a cibiyar sana'o'i ta Amurka, ta ce wani karni na tafiyar hawainiya da bunkasar harkokin samar da hajoji da hidima ke fuskanta, zai yi mummunan tasiri ga rayuwar al'ummar duniya.

Christine Lagarde ta ce karuwar adadin mutane da shekarunsu ya ja da jan kafa da harkokin cinikayya na duniya ke yi da kuma rashin warware gadon matsalolin kudi na duniya, su ne manyan kalubale da bunkasar harkokin samar da hajoji ke fuskanta.

Ta ce domin magance matsalolin, IMF ya yi kira da a dauki matakan rage yanayin rashin tabbas domin bunkasa harkokin zuba jari a harkokin samar da ababen more rayuwa mafiya kawo riba.

Lagarde ta kara yin kira da a kara inganta horo da ilimantarwa a fannin daga matsayin riba da ake samu da rage rashin daidato. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China