in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawar Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na Amurka Donald Trump
2017-04-06 13:14:57 cri

Sannin kowa ne alaka tsakanin Sin da Amurka na da dadadden tarihi na shekaru masu yawa. Bisa tarihi tun cikin shekarar 1844 Amurka ta amince da matsayin kasar Sin na kasa mai cin gashin kanta, duk da cewa bayan hakan an rika samun yankewar huldar bisa wasu dalilai.

Idan kuwa aka kalli matsayin dangantakar wadannan kasashe a duniyar yanzu, za a ga cewa kasashen biyu su ne ke kan gaba wajen ci gaban tattalin arziki a duniya baki daya, kaza lika Sin ita ce kasa ta biyu a duniya wajen baiwa Amurka bashi, in ban da kasar Japan dake lamba daya a wannan fanni.

A 'yan shekarun baya baya na nan alakar sassan biyu ta kara samun kyautatuwa, bisa tattaunawa, da mu'amala dake wanzuwa tsakanin shugabanni da jagororin kasashen biyu, musamman ta fuskar siyasa, da tattalin arziki, da tsaro, da yaki da ta'addanci, da kuma kokarin yaki da yaduwar muggun makamai na kare dangi.

Baya ga matsayin Sin da Amurka na manyan kasashe dake ingiza tattalin arzikin duniya gaba daya, kasashen na taka muhimmiyar rawa wajen habaka tsaro a sassan duniya, bisa matsayinsu na mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD. Har ila yau suna zama wani ginshiki na hadin gwiwa, a duk lokacin da ake batu na raya hadin gwiwa, ko bunkasa ci gaban kasa da kasa, ko shiyya shiyya, da ma fadin duniya baki daya.

A kuma wannan gaba da ake sa ran ganawar shugaba Xi Jinping na kasar Sin da Mr. Donald Trump na Amurka, hankula na karkata ga irin tasirin da wannan zantawa za ta haifar, musamman ganin yadda kasashen biyu suke da sabanin ra'ayi kan wasu manufofi na mulki da na tattalin arziki. Wasu batutuwa da masharhanta ke ganin na iya janyo hankalin sassan biyu, sun hada da batun jibge na'urorin THAAD a yankin zirin koriya wanda ke samun goyon bayan Amurka. Sai kuma batutuwan cinikayya dake tsakanin sassan biyu, da batun tsaro a Koriya ta Arewa, da manufofin yaki da tasirin sauyin yanayi da dai sauransu.

Ranar 6 da 7 ga watan Afrilu ne dai aka tsayar, a matsayin ranekun da shugabannin na Sin da Amurka za su gana da juna a Mar-a-Logo dake jihar Floridan kasar Amurka. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam/ Sanusi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China