in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarauniya Elizabeth ta sanya hannu kan dokar ficewar Birtaniya daga EU
2017-03-16 20:09:00 cri
Sarauniya Elizabeth ta Birtaniya, ta sanya hannu kan dokar Brexit, wadda ta tanaji ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai ta EU, matakin da a yanzu haka ke nuna cewa, firaministar kasar Theresa May, na da damar ci gaba da tattaunawa game da wannan manufa ta ficewar Birtaniya daga EU.

Kakakin majalissar dokokin kasar John Bercow, ya shelanta a Alhamis din nan cewa, kudurin dokar ficewa daga EU, ya samu amincewar sarauniya, bayan da majalissar ta zartas da shi a ranar Litinin.

Yanzu haka dai firaministar Birtaniya za ta sanar da hedkwatar EU aniyar Birtaniya ta barin kungiyar, tare da tsare tsare na shekaru 2 da za a aiwatar gabanin hakan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China