in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Burundi sun tattauna kan kara fadada dangantaka a tsakanin kasashen biyu
2017-03-16 09:09:37 cri

Kasashen Sin da Burundi sun amince su kara fadada hadin gwiwa a tsakaninsu, wannan na zuwa ne bayan ganawar da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka yi jiya Laraba a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

A jawabinsa yayin ganawar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan matakan da Burundi ke dauka na bunkasa kasarta, kuma a shirye kasar Sin ta ke ta karfafa hadin gwiwa da kasar ta Burundu a fannonin aikin gona, da samar kayayyakin more rayuwa, da inganta rayuwar al'umma da sauran su.

Wang Yi ya bukaci kasashen biyu da su kara fadada hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin musayar al'adu da al'ummominsu, da kara hada kai a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nasa jawabin, ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Burundi Alain Aime Nyamitwe ya ce, gwamnatin kasarsa za ta hada kai da kasar Sin don ci gaba da goyon bayan juna kan muradunsu gami da sauran muhimman batutuwa.

Ya kuma gayyaci kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar Burundi. Daga bisana bangarorin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar tuntubar juna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China