in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firayiministan kasar Sin: Amurka da Sin na tattaunawa game da ganawar shugabannin kasashen biyu
2017-03-15 11:33:34 cri

Firayiministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce Amurka da Sin na tattaunawa game da ganawar da Shugaba Xi Jinping zai yi da takwaransa Donald Trump.

Da yake jawabi ga taron manema labarai bayan kammala zaman majalisar dokokin kasar na shekara-shekara a yau Laraba, Li Keqiang ya ce tuni ofisoshin jakadancin kasashen biyu suka fara tattaunawa game da ganawar gaba da gaba da shugabannin biyu za su yi.

Ya ce dangantaka tsakanin Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, ba kadai ga kasashen ba, har ma da yankunansu da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali na duniya baki daya.

A don haka, ya ce dole su yi aiki tare wajen inganta wadannan abubuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China