Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kana shugaban rundunar askarawar kasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilai daga rundunar 'yantar da jama'a ta kasar Sin (PLA) yayin taron shekara-shekara na majalisar jama'ar kasar Sin. Ya kuma bayyana cewa, ya kamata a kara himma wajen taimakawa sojojin kasar da fasahohin kimmiya da kirkire-kirkire na zamani. (Ibrahim Yaya)