in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunisiya, Masar da Aljeriya sun sake watsi da warware rikicin Libya ta hanyar matakan soja
2017-02-21 10:29:14 cri

A jiya Litinin 20 ga watan nan ne a birnin Tunis, ministocin harkokin wajen kasashen Tunisiya, da Masar da Aljeriya, suka sake nanata kin amincewar su da daukar makatan soji, wajen warware rikicin kasar Libya, suna masu cewa hanyar Siyasa ce hanya daya kacal da za iya bi domin warware rikicin kasar.

A wannan rana, ministocin kasashen 3, sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa bayan kammala shawarwarin su, inda suka jaddada cewa, al'ummar kasar ta Libya ne kawai ke da ikon warware batun kasarsu da kansu.

Sanarwar ta kuma nuna kin amincewa, da sauran kasashen duniya su tsoma baki cikin batun kasar ta Libya ta hanyar matakan soja, sa'an nan ta jaddada cewa, kamata ya yi sassa daban daban su girmama "yarjejeniyar siyasa ta kasar Libya".

Ban da haka kuma, sanarwar ta ce, an tsai da kudurin kiran taron shugabannin kasashen Tunisiya, da Masar da Aljeriya a birnin Algiers, hedkwatar kasar Aljeriya nan ba da dadewa ba, inda za su tattauna yadda za a warware batun kasar ta Libya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China