in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tuntubi Indiya dangane da batun Taiwan
2017-02-15 20:14:02 cri

A Larabar nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa Sin ta riga ta tuntubi kasar Indiya a hukumance, dangane da batun yankin Taiwan.

Geng Shuang ya fadi haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya ce kasar Sin na fatan Indiya za ta bi manufar "kasar Sin daya tak a duniya", za kuma ta yi taka tsan-tsan yayin da take daidaita batun Taiwan.

An labarta cewa, yanzu haka 'yan majalisar kafa dokokin yankin Taiwan 3 na ziyara a kasar Indiya, inda kuma suka gabatar da shawarar "daga matsayin hukumar Taiwan da ke Indiya". (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China