Shugaban wanda ya yi furucin yayin wani taron manema labaru na hadin gwiwa da firaministan kasar Japan Shinzo Abe, da aka kira a fadar White House, ya ce shi da takwaransa na kasar Sin sun tattauna abubuwa da dama.
A cewar shugaban kasar Amurka, akwai kyakkyawar huldar tsakanin Amurka da Sin, kuma Amurka na cikin muharawa da kasar Sin kan batutuwa daban-daban.
Ya ce, yadda ake samun kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen 2, zai amfanawa daukacin kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasific, da suka hada da Amurka da Sin da kuma Japan.
Kafin haka, fadar White House ta Amurka, ta ba da sanarwa a ranar 9 ga wata cewa, shugaba Trump da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping sun zanta da juna ta wayar tarho a ranar, inda suka dade suna tattauna abubuwa da yawa.
Kuma cikin zantawar ne, shugaba Trump ya amince da bin manufar "kasar Sin daya tak a duniya".
Shugabannin 2 dai, sun share fagen muhawarar da za a yi tsakanin kasashen 2 kan batutuwa da dama da suka shafi moriyarsu ta bai daya.(Bello Wang)