in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 35 sun mutu a harin ta'addanci a Istanbul
2017-01-01 12:10:06 cri
Gwamnan Istanbul Vasip Sahin, ya ce a kalla mutane 35 ne suka mutu, kana wasu mutune 40 suka jikkata a sakamakon harin da aka kaddamar a wani shahararren gidan rawa da safiyar yau Lahadi a Istanbul.

Sahin ya ce wani dan bindiga ne ya kaddamar da harin shi kadai.

Wani mai sharhi kan al'amurran tsaro wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharin ya harbe mai gadin gidan rawar, daga nan kuma ya kutsa kai gidan rawar inda ya bude wuta, wajen na cike makil da jama'a sama da mutane 400 wadanda ke gudanar da bikin murnar zuwan sabuwar shekara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China