in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liverpool da Napoli na zawarcin dan wasan bayan Brazil
2016-12-28 19:11:49 cri
Rahotannin kafafen yada labaru sun rawaito cewa, Liverpool da Napoli na daga cikin kungiyoyin wasannin dake neman amincewar gwarzon dan wasan baya na kasar Brazil Thiago Maia ya sanya hannu kan yarjejeniyar aiki da su.

Dan wasan mai sheakru 19 a duniya, wanda ya kulla kwantiragi da kungiyar wasan kwallon kafan ta Santos na kasar Brazil wanda zata kare a watan Yunin shekarar 2019, rahotanni sunce masu zawarcin dan wasan sun hada da Monaco, Schalke da Zenit Saint-Petersburg, da kuma Sambafoot.

Maia yace zai yanke hawara game da makomar rayuwarsa ne a ranar 11 ga watan Janairu bayan ya dawo daga hutu.

"Santos da wakilaina zasu yanke shawara idan har lokacin hakan yayi", inji dan wasan tsakiyar.

Maia ya bayyana a kungiyar wasan a karon farko ne sau 91, tun bayan da ya fara aiki da Santos a shekarar 2014. Ya kuma wakilci kasar a wasannin yan kasa da shekaru 17, dana yan kasa da shekaru 20 da kuma matakina 23 l, kuma yana daga cikin rukunin yan wasan da suka yi nasarar lashe gasar zinare a wasannin Rio Olympics a watan Augusta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China