in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Haduwa a kantin sayar da kofi na "Huayuanli" don kara fahimtar birnin Quanzhou
2016-12-28 08:16:17 cri

Wani abu da ya wuce zaton Jin Xu shi ne, bayan shekara guda kawai, shi da abokan arzikinsa biyu wato Hupan da Lin Xiaodong sun kaddamar da wani kantin sayar da kofi wato Huayuanli a titin Xijie.

"kafin ya canja zuwa wani titin kasuwanci, ana iya gudanar da duk abu mai ban sha'awa da kake so a fannin zane."

Titin Xijie wata tsohuwar unguwa ce da aka kiyaye al'adun gargajiya sosai a birnin Quanzhou, wanda ke da tarihi na fiye da shekaru dubu daya, inda ake kuma iya samun dimbin tsoffin gine-gine. A yayin daular Song wato daga shekarar 960 zuwa ta 1279,Titin Xijie wata alama ce ta wadatar Quanzhou. A lokacin hutu na watan Oktoba na shekarar 2015, ko da yake babu tallace-tallace, amma akwai dunbun masu yawon shakatawa da suke kwarara zuwa Quanzhou don yawon bude ido. Lamarin da ya sa Hu Pan, wata 'yar lardin Hunan ta gano zarafin kasuwanci a birnin.

"Quanzhou na da al'adun gargajiya mai dogon tarihi, ana iya samun wasan kwaikwayo na gargajiya iri daban daban a nan, don haka ina zaton cewa, kayayyakin al'adu za su iya samun karbuwa a kasuwa."

Yayin da take waiwaye a karon farko game da zuwanta Quanzhou, Hu Pan ta bayyana cewa, a wancan lokaci bata fahimci Quanzhou sosai kamar yadda ta fahimceshi a yanzu ba. Bisa la'akari da yadda wajen ibada na mabiya addinin budda da masallaci suke makwataka da juna, kana da tsoffin gine-gine da dakunan duwatsu suke kasancewa cikin halin jituwa, Hu Pan ta yi mamaki sosai, kuma ta fara nuna sha'awa ga birnin. Gaskiya dai Quanzhou ya burge ta kwarai da gaske, in ji ta.

Da ma Hu Pan na da aniyar zama a Quanzhou ne don bude wani kantin tsara bikin aure, amma bayan da ta gamu da mijinta Lin Xiaodong, ta tsai da kuduri wajen kafa wani kantin sayar da kofi.

"Da ma ni mutum ne mai tsara fasali ga kananan otel-otel, kuma na taba yin dimbin fasalolin irin hakan. Amma ko da yaushe ina da wata aniyar tsara fasali ga otel dina."

Kwarewar da mijinta Lin Xiaodong ya nuna wajen tsara fasali ta bai wa Hu Pan karfin gwiwa sosai wajen cimma burinta na kafa wani kantin sayar da kofi. Don haka ta nemi abokinta Jin Xu, ta kuma gaya masa wannan kuduri nata, wanda ya samu goyon baya sossai daga wajen Jin Xu.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China