Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya mika sakon ta'aziyya ga sakatare na farko na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba, Raul Castro, inda a madadin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar da jama'ar kasar da kuma shi kansa, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan rasuwar Fidel Castro, tare da nuna ta'aziyya ga iyalansa.
A sakon da ya aika, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Fidel Castro ne ya kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba da kuma sha'anin gurguzu na kasar, haka kuma jagora ne na al'ummar kasar, wanda ya sadaukar da duk rayuwarsa ga harkar 'yantar da jama'ar kasar ta Cuba, da kuma kiyaye mulkin kan kasar da raya harkokin gurguzu a kasar, ya ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar harkokin gurguzu a duniya, shi babban mutum ne a wannan zamaninmu, wanda za a rike shi a tarihin duniya.
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ma ya mika sakon ta'aziyya ga Raul Castro.
Har wa yau, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ma ya mika ta'aziyyarsa kan rasuwar Fidel Castro, inda a cikin sakonsa ya bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar alama ta tarihin duniya na zamani.
Sai kuma a sanarwar da fadar mulki ta White House ta kasar Amurka ta fitar a jiya Asabar, gwamnatin Amurka ta nuna jaje ga iyalan Castro, kuma ta bayyana cewa, tarihi zai rike tare da tantance babban tasirin da Castro ya kawo wa jama'ar Cuba da kuma duniya baki daya.
Baya ga haka, shugabannin kasashen Faransa da Bolivia da Venezuala da Mexico da Ecuador da kuma Uruguay su ma sun mika sakwannin ta'aziyya kan rasuwar Castro.(Lubabatu)