in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Cuba ta sanar da zaman makoki na kwanaki 9 don nuna juyayi ga rasuwar Fidel Castro
2016-11-27 13:21:17 cri

A safiyar jiya Asabar, gwamnatin kasar Cuba ta sanar da fara zaman makoki na kwanaki 9 don nuna juyayi da alhini ga rasuwar shugaban juyin juya halin kasar Fidel Castro.

Jaridar Granma, wato jaridar jam'iyyar kwaminis ta Cuba ta ba da labari cewa, gwamnatin kasar ta sanar da cewa, daga ranar 28 zuwa 29 ga wata, jama'a zasu iya zuwa wajen dutsen tunawa na José Martí dake Havana babban birnin kasar don nuna juyayi ga Fidel Castro. Baya ga haka, a daren ranar 29 ga wata, za a shirya wani taron jama'a, don nuna girmama ga Gastro.

Fidel Castro ya riga mu gidan gaskiya a ranar 25 ga wata da dare, da karfe 10 da minti 29, yana da shekaru 90 a duniya.

An haifi Castro a ranar 13 ga watan Agusta na shekarar 1926. A watan Janairun shekarar 1959, ya jagoranci 'yan tawaye wajen tumbuke mulkin kama karya na Fulgencio Batista, tare kuma da kafa gwamnatin juyin juya hali, daga baya kuma ya rike kujerun firaminista, da babban kwamandan rundunar sojoji. A shekarar 1976, Castro ya dare kujerar shugaban majalisar gudanarwa. A shekarar 2006, ya mika mulki ga Raúl Castro sakamakon rashin lafiyar jiki, tun daga lokacin ya rage fitowa gaban jama'a. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China