in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda zata yi sansani a Dubai a domin tunkarar gasar 2017 AFCON
2016-11-16 15:58:22 cri
Kungiyar kwallon kafan Uganda Cranes, zata buga wasanni masu yawa a Dubai gabanin shiga gasar wasannin kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato 2017 (AFCON) a shekara mai zuwa, bayan shafe shekaru 39 bata samu damar shiga gasar ba.

Shugaban tawagar yan wasan kasar ta Uganda Milutin Sredojevic, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kungiyar wasan ta shirya tinkarar manyan kungiyoyin wasannin, kuma zasu yi kyakkyawan amfani da irin kwarewar da suka samu a lokacin bada horon domin shiga gasar kwallon kafa mafi girma ta nahiyar Afrika wanda za'a gudanar a kasar Gabon.

Uganda ta samu nasarar shiga gasar ta 2017 AFCON ne, bayan da ta doke Comoros da ci 1-0 a wasannin da suka buga a a watan jiya, bayan da kasar ta shafe shekaru 39 ba tare da shiga gasar ba. Kungiyar wasan ta Cranes, ta buga wasanta na karshe ne a shekarar 1978, bayan data kwashi kashinta a hannun Ghana mai masaukin baki da ci 2-0 a wasan karshe.

Cranes wacce ke a zaune a Port Gentil a lokacin gasar ta AFCON a Gabon, tana rukuni daya da kasashen Masar, Ghana da Mali.

Uganda ce kasa daya tilo cikin kasashen gabashi da tsakiyar Afrika da kungiyar wasan kwallon kafarta ta samu nasarar shiga gasar wasannin kwallon kafa ta 2017 AFCON, wanda za'a gudanar a badi.

Hukumar kula da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Uganda tuni ta gabatar da kasafin kudi na dala miliyan guda ga gwamnatin kasar, wanda zata yi amfani da kudaden wajen horas da yan wasanta a Dubai, da kuma gudanar da al'amurran gasar wasannin ta AFCON.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China