Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya bar birnin Niamey jiya Litinin domin isa birnin Addis Abeba na kasar Habasha, inda zai halarci wani taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na kwamitin koli na kasashen dake makwabtaka da Libya, in ji wata sanarwar fadar shugaban kasar Nijar.
Wannan haduwa ta zo wata guda bayan taron wanda ministocin harkokin wajen kasashen dake makwabtaka da Libya suka yi a Niamey, babban birnin kasar Nijar, a gaban idon wakilin musamman na sakatare janar na MDD game da kasar Libya, mista Martin Kobler, da tsohon shugaban Tanzaniya, manzon musammun na kungiyar tarayyar Afrika (AU) game da kasar Libya, mista Jakawa Kikwete, duk kan wannan batu guda na rikicin Libya. (Maman Ada)