Fiye da ton hudu ne na miyagun kwayoyin da aka kama da suka hada da ton 3.4 na tabar wiwi, kilogram 500 na miyagun kwayoyin, gram 435 na hodar iblis duka aka kona su a ranar Laraba a birnin Bamako a karkashin jagorancin babbar hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar Mali (OCS). Wadannan miyagun kwayoyin da aka kiyasta darajarsu zuwa kudin Sefa miliyan dari biyar, an kama a cikin wasu ayyukan daban daban da aka gudanar tun farkon wannan shekarar dake muke ciki. (Maman Ada)