in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tsara zamanantar da aikin gona nan da shekarar 2020
2016-11-03 16:29:46 cri

Majalisar zartaswar kasar Sin ta gabatar da wani sabon shiri na shekaru biyar wanda ke bayyana kudurin gwamnatin kasar Sin na zamanintar da aikin noma a dukkanin fadin kasar nan da shekara ta 2020.

Manufar tsarin ita ce samar da isasshen abinci, da tabbatar da ingancin kayayyakin abincin da ake samarwa a fadin kasar ta Sin, tare da karfafa gogayyar kasar ta fuskar samar da abinci a duniya nan da shekara ta 2020.

Har wa yau tsarin zai baiwa mazauna yankunan karkarar kasar Sin damar gudanar da ingantacciyar rayuwa daidai wa daida, za kuma a yi amfani da tsarin wajen kafa cibiyoyin gwajin ayyukan gona na zamani a sassa daban daban na kasar.

Kaza lika, tsarin zai taimaka wajen inganta ayyukan kirkire-kirkire, da na gudanarwa, tare da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, baya ga batun bude kofofin ci gaba ga manoma.

Masu sharhi na bayyana wannan mataki a matsayin babban ci gaba a kokarin da mahukuntan kasar Sin ke yi na inganta rayuwar al'ummarta daga dukkan fannoni, kasancewar "Noma shi ne tushen arziki" (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China