in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin yanayin kiwon lafiyar kasar Sin: matsakaicin shekarun Sinawa zai kai 79 nan da shekarar 2030
2016-10-27 13:20:46 cri

Kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS da majalisar gudanarwar kasar sun bullo da wani shirin kiwon lafiya, shirin da ke nuna cewa, nan da shekarar 2030, Sinawa za su kara samun ci gaba a fannin kiwon lafiya kamar na sauran kasashe masu cigaba, kana matsakaicin shekarun haihuwa na Sinawa zai kara shekaru 3, wanda zai kai 79. Yawan mutanen da suke motsa jiki ya karu daga miliyan 360 a shekarar 2014 zuwa miliyan 530 a shekarar 2030. Kana Sin za ta kara inganta fasahohinta na likitancin gargajiya, domin kara rawar da wannan fannin yake takawa a fannin warkar da cututtuka dake addabar jama'a sannu a hankali. Bayanai na nuna cewa, wannan shiri shi ne irin sa na farko da kasar Sin ta bullo da shi a fannin kiwon lafiya na matsakaici da kuma dogon lokaci tun bayan da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Shirin ya kuma tanadi burin da ake fatan cimmawa a fannin inganta harkokin kiwon lafiya nan da shekarar 2030, matsakaicin yawan shekarun haihuwa na jama'a zai karu zuwa 79, kana za a samu raguwar jarirai da yara 'yan kasa da shekaru 5 da kuma mata masu juna biyu da ke mutuwa. Yawan mutanen da suke motsa jiki zai karu daga miliyan 360 a shekarar 2014 zuwa miliyan 530 a shekarar 2030. Yawan mutanen da suka mutu tun suna kuruciya a sakamakon cututtuka masu tsanani zai ragu da kashi 30 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2015, kana yawan kudin da ake kashewa a fannin jinya cikin kudin da ake kashewa a fannin kiwon lafiya zai ragu daga 29.3 cikin dari zuwa 25 cikin dari.

Bugu da kari, shirin ya gabatar da cewa, yawan ranakun dake da ingancin iska zai kai fiye da kashi 80 cikin dari kafin shekarar 2020. Za a ci gaba da kyautata wannan hali ne har shekarar 2030. Yawan ingancin ruwa da aka iya yin amfani da shi zai karu zuwa kashi 70 cikin dari nan da shekarar 2020. Sannan kuma za a rika kyautata wannan hali har zuwa shekarar 2030. Ban da haka kuma, a shekarar 2030, za a kara tsarin sa ido kan ingancin abinci a dukkan fannoni.

Shugaban sashen koyon ilmin kiwon lafiyar jama'a na kwalejin koyon ilmin likitanci na Peking Union Liu Yuanli ya bayyana wa manema labaru cewa, wannan shirin da aka gabatar wani muhimmin mataki ne na tabbatar da kiwon lafiyar jama'a. Ya ce,

"An tsara shirin kiwon lafiya na kasar Sin ne domin mai da martani ga halin da kasarmu ke ciki a fannin kiwon lafiya, kuma ya zuwa yanzu mun samu sakamako mai kyau a wannan fanni, matsakaicin yawan shekarun haihuwa na mutane ya kai 76.34 a shekarar 2015, wanda yake kan gaba a cikin kasashe masu tasowa. Amma duk da haka, muna ci gaba da fuskantar kalubale da dama, a saboda haka, ya kamata mu ci gaba da tinkarar cututtuka masu tsanan dake addabar mutane sannu a hankali."

A cikin wannan shiri, an kara sanya ido kan yadda za a inganta lafiyar jama'a a maimakon yadda za a warkar da mutane bayan da suka kamu da cuta. A halin yanzu, an kara la'akari da yanayi da kuma muhallin da jama'a suke rayuwa, domin kyautata lafiyar mutane a dukkan fannoni. Shugaban cibiyar nazarin yada ilmin kiwon lafiya ta jami'ar Fudan Fu Hua ya bayyana cewa,

"Akwai abubuwa da yawa da suke yin tasiri ga kiwon lafiyar mutane, alal misali, muna kira da a rage shan taba, sannan a rika cin abinci masu inganci da kuma kara motsa jiki. Sai dai kuma ba za mu iya tilasta wa mutane ko tsara musu yadda za su tafiyar da rayuwarsu ba. A saboda haka, muna bukatar taimakon sassa daban daban na al'umma domin cimma wannan buri, ciki har da wasu hukumomin kasuwanci."

Ban da wadannan kuma, domin rigakafin cututtuka masu tsanani dake addabar jama'a sannu a hankali, shirin ya gabatar da cewa, ya kamata a kara inganta fasahohin jinya na gargajiya na Sin domin kara kyautata rawar da suke takawa a wannan fanni. Haka kuma ya kamata a kara inganta aikin ba da hidimar jinyar gargajiya ta Sin, da bullo da tsarin ba da irin wannan hidima a dukkan birane da kauyuka, a kokarin da ake yi na cimma burin rage yawan mutane da suke mutuwa tun suna kuruciya a sakamakon irin wadannan cututtuka. (Lami Li)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China