in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu game da himmar Victor Moses inji Mikel Obi
2016-10-19 15:42:53 cri
Dan wasan Super Eagles John Obi Mikel, ya yaba wa kwazon takwaransa Victor Moses, game da irin rawar gani da yake takawa a kungiyar Chelsea da suke bugawa kwallo tare. Obi ya ce Moses ya gwada kwarewar sa a wasan da Chelsea din ta doke Leicester City da ci 3 da nema.

Kwallon da Moses din ya ciwa Chelsea a wannan wasa ita ce ta biyu, da ya zura a raga a gasar Firimiya ta bana, sai dai duk da hakan Obi na ganin nan gaba kadan, dan wasan zai samu cikakken gurbi a kungiyar, bayan da a baya ya bugawa kulaflikan Liverpool, da Stoke City wasa a matsayin dan wasan aro.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China