Gwamnatin Najeriya ta yi karin haske game da rade-radin da ake bazawa cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun sako 'yan matan sakandaren garin Chibok da ke hannunsu ne, bayan da aka saki wasu daga cikin magoya bayansu da ake tsare da su.
Ministan watsa labarai da al'adun Najeriya Lai Mohammed ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, wannan ba ya nufin an yi bani gishiri in ba ka manda .
Lai ya ce, sako 'yan mata 21 matakin farko ne a kokarin da gwamnati ke yi na ganin an sako baki dayan 'yan matan da kungiyar ta ke tsare da su. A cewarsa, sako wadannan 'yan mata wata alamar yarda ce a tattaunawar da bangarorin biyu suke yi game da sako 'yan matan.
Ministan ya ce, bayan da 'yan matan suka iso Abuja, an tanadi likitoci, da masu binciken lafiyar kwakwalwa da ma'aikatan agaji da sauran kwararru a bangaren lafiya domin duba lafiyar yaran, saboda tsawon lokacin da suka dauka suna tsare a hannun 'yan ta'addan. Haka kuma, gwamnati ta tattara sunayen 'yan mata 21n da aka sako, inda ake shirin tuntubar iyayensu domin su tabbatar da cewa, 'yayansu ne.
A farkon wannan watan ne dai, gwamnatin Najeriya ta ce, za ta ci gaba da lalubo dukkan hanyoyin da suka wajaba na ganin an sako 'yan matan na Chibok. Sau uku dai mahukuntan Najeriyar ke kokarin ganin an sako yaran, amma hakan ya faskara.
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne, 'yan Boko Haram din suka yi awon gaba da 'yan mata 214 a makarantarsu da ke garin Chibok a jihar Borno. Tun bayan shekaru biyu da sace wadannan 'yan mata, guda 57 ne kawai suka kubuta, kuma har yanzu ba a ji duriyar 219 daga cikin su ba.
Ko da yake a watan Mayun wannan shekara, daya daga cikin 'yan matan ta kubuta tare da 'yar da ta haifa yayin da ta ke tsare a hannun 'yan Boko Haram.(Ibrahim)




