in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta shirya bikin aza harsashin wani aiki da kasar Sin ta tallafa
2016-09-29 09:35:24 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU ta shirya wani bikin aza harsashin aikin wani katafaren gini da kasar Sin ta samar.

Aikin wanda gwamnatin kasar Sin ta dauki nauyinsa zai kunshi na'urorin tantancewa, dakin cin abinci da cibiyar adana muhimman bayanai da na baje kolin kayayyaki.

A jawabinta yayin kaddamar da bikin da ya gudana a cibiyar kungiyar da ke birnin Addis Ababan kasar Habasha, shugabar hukumar zartarwar kungiyar Madam Nkosazana Dlamini Zuma, ta ce, kayayyakin da za a sanya a cikin wannan cibiya, za su taimakawa kungiyar ta AU a lokutan tarukan ta koli, da sauran taruka yadda ya kamata. Haka kuma za a baje kolin kayayakin tarihin kasashen Afirka da wasu muhimman rubuce-rubucen da kungiyar da kuma wasu kwararrun hukumomin ta suka gabatar a katafaren ginin.

Uwar gida Zuma ta yaba irin taimakon da mahukuntan kasar Sin suke baiwa ayyukan kungiyar, matakin da ke kara hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar AU Kuang Weilin, ya bayyana cewa, taimakon baya-bayan nan da kasar Sin ta samarwa kungiyar ta AU, wata alama ce da ke kara nuna kyakkyawar alakar da ke wanzuwa tsakanin Sin da Afirka. Ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka suna da damammaki da dama na hadin gwiwa.

Mr Kuang ya sake nanata kudurin kasar Sin na nuna goyon baya ga kasashen Afirka a ko wane lokaci, a kokarin da ake na aiwatar da ajandar da aka tsara da nufin gina dunkulalliyar nahiyar Afirka mai cike da makoma mai haske da kuma zaman lafiya.

Wannan gini da kasar Sin za ta samar, wata dama ce ta nuna kayayyakin tarihin tsoffin shugabannin nahiyar, da gwagwarmayar kwatar 'yan cin da al'ummun Afirka suka yi da kokari da kuma nasarorin da kungiyar AU ta cimma.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China