in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Najeriya ya fuskanci koma baya
2016-09-07 15:13:56 cri

Wani saban rahoto da aka wallafa a kwanakin baya kan sabbin alkaluman tattalin arzikin Najeriya ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya yi lalacewar da ba a taba ganin irinta ba cikin kusan shekaru 10. Amma kuma gwamnatin kasar ta ce har yanzu tana hango haske kan makomar kasar a nan gaba.

Duk da halin kunci da al'ummar kasar suka cintsi kansu a ciki a wannan shekarar, kadan daga cikin 'yan kasar ne dai suka yi tsammanin girman matsala ga tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal. To sai dai kuma wani rahoton zango na biyu na hukumar kiddidigar kasar ya ce, lamarin tattalin arzikin kasar ya kara lalacewa inda ya samu gibin da ya kai na kaso 2,06 cikin dari a watanni uku kacal.

Sai dai gwammatin Najeriyar ta ce tana daukar matakan da suka dace na ganin ta inganta bangaren tattalin arzikin kasar da bai shafi man fetur ba, da kuma dawo da darajar kudin kasar wato Naira da yanzu haka ya durkushe.

To sai dai a cewar masana tattalin arziki, shi kansa rahoton yana nuna alamar sauyin da ke shirin amfanar kasar cikin dan kankanin lokaci.

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya yi hasashen yiwuwar koma baya da ta kai ta kaso 1,8 na tattalin arzikin kasar a karshen shekarar. Masana na danganta wannan matsala da rashin masu zuba jari, sakamakon matsalar tsaro da ke damun kasar sanadiyar rikicin Boko Haram, da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, da karancin kudaden shigan kasar sanadiyar fasa bututan mai da 'yan tawayen Neja Delta ke haddasawa da sauransu.

Masu fashin baki na cewa, muddin Najeriya tana son fita daga wannan kangi, wajibi ne ta inganta tsaro don janyo masu sha'awar zuba jari daga katare da sauran matakan da za su farfado da tattalin arzikin kasar. (Saminu,Ada,Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China