A jiya Laraba da safe ne, wani jirgin saman kamfanin JetBlue na kasar Amurka samfuri A320 ya tashi daga jihar Florida zuwa filin saukar jiragen sama na Santa Clara na kasar Cuba, abin da ya alamanta cewa an sake dawo da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Amurka da Cuba bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen sama ta tsawon fiye da shekaru 50 .
Kamfanin JetBlue ya ba da labari cewa, jirgin saman yana dauke da fasinjoji fiye da 150 ciki hadda sakataren sufuri na kasar Amurka. Rahotanni na cewa, tun daga jiya zuwa ran 29 ga wata Oktomba, ana saran za a rika jigilar mutane ta jiragen sama tsakanin Amurka da Cuba sau uku a ko wani mako, daga baya kuma jiragen za su rika tashi ne sau daya a ko wace rana.
Tun daga lokacin da kasar Cuba ta yi nasara a juyin juya hali a shekarar 1959, Amurka ta kan dauki matakan yin fito-na-fito da Cuba, inda suka yanke huldar jakadanci tsakaninsu a shekarar 1961. A shekarar 1962 kuma, tsohon shugaban Amurka na wancan lokaci John Fitzgerald Kennedy ya zartas da dokar yanke hulda da Cuba ta fuskar tattalin arziki, hada-hadar kudi da zirga-zirgar kasuwanci. Daga bisani kuma, a watan Disamba na shekarar 2014, kasashen Amurka da Cuba suka sanar da maido da dangatanka a tsakaninsu. A watan Yuli na shekarar 2015 kuma suka farfado da dangantakar diplomasiyya tsakaninsu. (Amina)