Babban sakataren asusun bunkasa harkokin man fetur (PTDF) Galadima Aminu ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron shekara-shekara game da nazarin harkokin mai da iskar gas na shekara ta 2014 da 2015.
Ya ce, binciken baya-bayan nan da aka gudanar a Lagos da yankin tafkin Chadi, ya kara bayyana kyakkyawar fatan da ake da ita na gano dimbin man da ke kwance a Najeriya, adadin da zai iya bunkasa yawan man da kasar take ajiyewa.
Babban sakataren na PTDF ya yi kira ga kamfanonin na gida da na kasa da kasa da su hada kai da masu bincike na Najeriya, ta hanyar samar musu da muhimman bayanai, kudade da kayayyakin aiki.
A cewarsa yin hakan zai taimaka musu wajen bullo da kayayyakin gudanar da bincike da ake bukata wajen bunkasa tattalin arzikin kasar da ma ci gaba mai dorewa. Bugu da kari, matakin zai karfafa musu gwiwa wajen ba da tasu gudummawar a kokarin da ake yi na warware wasu matsaloli da ke addabar bangaren masana'antun kasar, da samar da guraben ayyukan yi da musayar ilimi.
Asusun na PTDF dai ya bayyana kudurinsa na daukar nauyin masu bincike a fannin samar da mai da iskar gas ta hanyar amfani da tsirrai, inda tuni aka ware wasu kudade a wadannan fannoni. (Ibrahim)




