Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana cewa,wannan mataki ya nuna irin kudurin da kasashen Sin da Kenya suka cimma na ganin bayan masu aikata munanan alaifuffuka a cikin kasashen biyu.
Wata sanarwa da ta rabawa manema labarai bayan da aka tuso keyar mutanen guda 40 a ranar Litinin, 35 daga cikinsu sun fito ne daga babban yankin kasar Sin, yayin da biyar daga cikinsu kuma suka fito daga yankin Taiwan, inda ake tsare da su a ofishin 'yan sanda.
A watan Afrilu ma an tuso keyar wasu mutane 77 da ake zargi daga kasar ta Kenya wadanda suka fito daga babban yankin kasar Sin da kuma yankin Taiwan zuwa nan kasar Sin.(Ibrahim)