in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron matasa na kasashen Sin da Afirka
2016-08-11 09:20:47 cri

A ranar Litinin 1 ga watan Agustan shekarar 2016 ne aka bude taron matasan kasashen Sin da Afirka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron da ya hallara wakilai 132 daga kasashe mambobin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka 44, wakilan MDD da ma'aikatan diflomasiya daga kasashen Afirka da ke birnin Beijing na kasar sin.

Bikin ya kunshi sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi tsakanin shugabannin matasan sassan biyu, baya ga musayar ayyuka tsakanin matasa 'yan kasuwa daga kasashen na Sin da Afirka.

Wakilan matasan na Afirka sun kuma ziyarci lardunan Hubei da Henan dake kasar Sin. Daga bisani kuma aka rufe taron a birnin Guangzhou.

Tsohon firaministan kasar Sin Wen Jiabao ne ya kaddamar da wannan dandalin yayin taron hadin gwiwar ministocin Sin da Afirka da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a watan Disamban shekarar 2003.

Idan kuma ba a manta ba, a lokacin taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da aka gudanar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a shekarar 2006. Kasar Sin ta yanke shawarar tura matasa masu aikin sa-kai guda 300 zuwa kasashen Afirka don ba da gudummawa a fannonin kiwon lafiya, aikin gona, wasanni, sana'o'in hannu, koyar da harshen Sinanci da sauransu.

Masu fashin bakin na cewa, wannan wani mataki ne mai fa'ida na kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni. Sannan wata dama ce ga matasan Afirka da ke halartar wannan taro wajen ganin irin ci gaban da matasan kasar Sin suka samu a fannonin rayuwa dadan-daban, da kuma matakan da ita kanta gwamnatin kasar Sin ta samar wa matasanta.

Bugu da kari, masana na cewa, akwai bukatar gwamnatocin kasashen Afirka su bullo da nagartattun hanyoyin inganta rayuwa da kafofin samun rancen kafa sana'o'i masu sauki ga matasan kasashensu. Da fatan matasan Afirka za su yi amfani da abubuwan da suka gani a lokacin wannan ziyara da suka kawo nan kasar Sin. (Saminu, Ada, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China