Ali Khamenei ya bayyana cewa, kamata ya yi Amurka ta gaggauta soke takunkumin da ta kakkaba wa Iran domin rayuwar jama'ar kasar ya kyautata, amma tun bayan watanni shida da suka gabata, har yanzu rayuwar jama'a a kasar ba ta canja ko kadan ba.
Ali Khamenei ya kara da cewa, Amurka ta keta yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma, tare da yunkurin bata dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da sauran kasashen duniya. Amurka ba ta cika nata alkawarin ba karkashin yarjejeniyar da aka cimma, wannan ya nuna cewa bai kamata a dogaro a kanta ba.
A watan Yulin bara ne, Iran da sauran kasashen shida da batun nukiliya na Iran ya shafa, wato Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin, da kuma Jamus suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a duk fannoni. An fara aiwatar da yarjejeniyar a watan Janairu na bana a hukunce. Bisa wannan yarjejeniya, MDD da kasashen yammacin duniya za su soke takunkumi da suka kakabawa wa Iran a fannin tattalin arziki idan Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya.
Amma har yanzu Amurka tana ci gaba da kakabawa Iran takunkumi bisa zarginta da laifin keta hakkin bil'adam da nuna goyon baya ga ta'addanci, yayin da Iran kuma ta musunta dukkan zargin da ake mata. (Fatima)