A shekarun baya, kasar Sin na kokarin raya jiragen kasa masu saurin tafiya, yanzu Sinawa suna iya tafiya zuwa yankunan kasar masu nisa cikin gajeren lokaci, yanzu, hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya sun hada manya ko matsakaitan birane da dama na kasar Sin. Ko shakka babu, hakan na canza zaman rayuwar jama'a sosai a kasar. Kana saurinsa da kuma fasahohinsa na kara kyautatuwa sosai.